logo

HAUSA

MDD ta nuna matukar damuwa game da karuwar masu rasa matsugunai a Sudan

2023-07-19 09:53:36 CMG Hausa

 

Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce dauki ba dadin da sassan da ba sa ga maciji da juna ke yi a kasar Sudan, na ta’azzara matsalar raba al’ummun kasar da muhallan su.

Dujarric ya ce MDD ta damu matuka da karuwar wannan adadi, inda alkaluman hukumar dake lura da bakin haure ko IOM, ke nuna cewa a makon da ya gabata, kusan mutane 200,000 ne suka kauracewa muhallan su a cikin kasar ta Sudan sakamakon yakin dake daidaita kasar. Ya ce matakan shawo kan yakin kasar Sudan na tattare da manyan kalubaloli.

Yanzu haka dai watanni 3 ke nan, tun bayan barkewar yaki a Sudan, kuma tuni yakin ya raba al’ummar kasar sama da miliyan 2.6 da matsugunan su. A hannu guda kuma, masu ayyukan jin kai na ci gaba da samar da tallafi ga ’yan kasar dake tserewa yakin.

Game da karuwar adadin masu tserewa daga kasar kuwa, hukumar lura da ’yan gudun hijira ta MDD, ta ce ya zuwa yanzu, adadin masu tserewa ta kan iyakokin Sudan zuwa kasashe makwafta ya kai kimanin mutum 730,000. (Saminu Alhassan)