logo

HAUSA

Putin ba zai halarci taron BRICS ba

2023-07-19 20:26:45 CMG Hausa

Rahotanni daga fadar shugaban kasar Afirka ta kudu na cewa, bisa yarjejeniyar da aka cimma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ba zai halarci taron kasashen BRICS ba.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce, ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ne zai wakilci kasar ta Rasha a taron. (Ibrahim)