logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a samar da ra'ayoyi daban-daban wajen raya harkokin gudanarwa na AI

2023-07-19 10:06:15 CMG Hausa

A jiya Talata ne wakilin kasar Sin ya yi kira da a samar da hadin kai tsakanin bangarori daban-daban a fannin raya harkar kirkirarriyar fasaha mai kwaikwayon tunanin dan adam (AI)

Zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya Zhang Jun ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da lamarin kirkirarriyar fasaha mai kwaikwayon tunanin dan adam (AI), cewa, duk da cewa lamarin AI ya kasance kamar harshen damo, kyan ta da rashin kyan ta ya danganta da yadda aka yi amfani da ita wajen daidaita ci gaba da tsaro.

Ya ce "Ya kamata al'ummomin kasa da kasa su tabbatar da hadin kai na gaskiya da juna, su shiga tattaunawa mai zurfi, da neman daidaito a kullum, da kuma gano ci gaban ka'idojin jagoranci na AI."

Ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana goyon bayan aikin daidaita tsarin Majalisar Dinkin Duniya a wannan fanni, kana tana goyon bayan kokarin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, wajen yin shawarwari masu zurfi a tsakanin bangarori daban daban, da kuma ba da cikakken hadin kai ga dukkan kasashe, musamman kasashe masu tasowa, wajen shiga wannan harka da kuma bayar da tasu gudunmawar.

Zhang ya jaddada ka'idar sanya da'a a gaba wajen raya AI.

Daidaita samun dama da amfani da kayayyakin fasahar AI da ayyuka na kasashe masu tasowa na da matukar muhimmanci wajen daidaita damar samun fasahar zamani, da ci gaba tsakanin kasashe masu arziki da marasa arziki. (Yahaya)