logo

HAUSA

Bunkasar Tattalin Arzikin Sin babbar nasara ce ga duniya

2023-07-19 09:18:17 CMG Hausa

A kwanaki baya ne, hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta tabbatar da cewa, mizanin GDPn kasar ya karu da kaso 5.5 bisa 100 a watanni shida na farkon shekarar 2023. 

Alkaluman hukumar ta NBS sun nuna cewa, a zangon farko na wa’adin, darajar GDPn Sin ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 59.3, kwatankwacin dalar Amurka kusan tiriliyan 8.3. Kazalika a rubu’i na biyu, GDPn ya bunkasa da kaso 6.3 bisa 100.

Kakakin NBS Fu Linghui, ya ce watanni shida na farkon shekarar nan, lokaci ne da sassan kasa da kasa suka sha fama da ayyuka masu sarkakiya na aiwatar da sauye-sauye, da samar da ci gaba da daidaito a cikin gida, kana dukkanin yankuna da sassan hukumomi sun yi matukar kokarin wanzar da daidaito, da samar da guraben ayyukan yi, da daidaita farashin hajoji.

Ya ce, sannu a hankali bukatun kasuwa na kara farfadowa, kuma ana samun karuwar samarwa da rarraba hajoji, da kara kyautatuwar sassan tattalin arziki. Alkaluman marasa aikin yi a kasar Sin ya tsaya kan kaso 5.3 a watanni 6 na farkon bana, kasa da kaso 0.2 kan na rubu’in farko.

Tun a watan Afrilu ne, hukumomin kasa da kasa kamar MDD da OECD, suka daga mizanin hasashensu game da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. 

Masu fashin baki na cewa, manufofi da tsare-tsaren kasar Sin game da raya tattalin arziki suna tasiri matuka, kuma hakan babban ci gaba ne ga duniya baki daya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi)