logo

HAUSA

National Interest: Dole ne kasashen yammacin duniya su shiryawa sakamkon da aka dade ana dako

2023-07-18 13:55:26 CMG Hausa

Wani rahoton Jaridar National Interest, ya ruwaito cewa, tsarin yammacin duniya da yadda ake raba iko tsakanin kasashe na gab da zuwa karshe, kuma dole ne kasashen yamma su yi kokarin gane cewa ba zai yuwu su ci gaba da nuna iko da duniya kamar a baya ba.

Rahoton wanda jaridar ta fitar a watan Yuni, ya kara da cewa, wasu muhimman abubuwa ne za su jagoranci sauyin da za a samu, wadanda za su tilastawa kasashen yamma fuskanta da rungumar yanayin da zai zo nan gaba, na raba iko da sauran kasashe, yana mai cewa, kin amincewa da hakan, ko yunkurin bigirewa, ka iya zama babban hadari ba kadai ga yammacin duniyar ba, har ma da kwanciyar hankalin duniya baki daya.

Za a iya kaucewa rikicin da ka iya barkewa, idan aka dauki wannan sauyi a matsayin dama ta gina duniya mai daidaito, maimakon matsayin matsalar da ke barazana ga wasu damarmaki ko gata na musamman. (Fa’iza Mustapha)