Kasar Sin Mai Fada Da Cikawa
2023-07-18 16:59:59 CMG HAUSA
DAGA FA’IZA
A karo na uku a dan tsakanin nan, wani babban jami’in Amurka na ziyara a kasar Sin. Sai dai a wannan karo, mai ziyarar shi ne jakadan Amurka mai kula da batun sauyin yanayi wato John Kerry. Ana sa ran yayin ziyararsa daga ranar 16 zuwa 19 ga wata, zai tattauna da bangaren kasar Sin kan batun sauyin yanayi, musamman game da yadda za a rage fitar da hayakin carbon a matsayinsu na kasashen da suka fi fitar da hayaki a duniya.
A ganina, ziyarar ta John Kerry ta zo a kan gaba, kuma a inda ya dace, la’akari da namijin kokarin da kasar Sin ke ci gaba da yi da zummar shawo kan matsalar.
Wani abu da na fahimta dangane da kasar Sin shi ne, ba ta daukar alkawarin fatar baki, ita mai fada da cikawa ce. Ina sa ran kasar Sin za ta cimma burinta na kaiwa matsayin koli wajen fitar da hayakin carbon a shekarar 2030, tare da a samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar da abubuwan da za su shawo kansa ya zuwa 2060. Tabbas tuni kasar Sin ta dau hanya domin ta dade da fara aiwatar da abubuwa, kamar dashen bishiyoyi da dazuzukan da kyautata jituwa tsakanin dan adam da muhallinsa da sarrafa shawa da amfani da kyautata amfani da makamashi mai tsafta da sauransu. Ina da yakinin Sin za ta cimma burinta kafin lokacin da ta ayyana.
Kuma na lura cikin dukkan wasu ayyukan kasar, ta kan mayar da hankali ne wajen ganin ta rage fitar da hayakin da ma duk wani abu da ka iya gurbata muhalli. Wannan ya tuna min da ziyarata ta baya-bayan nan a birnin Chengdu na lardin Sichuan, wato birnin da zai karbi bakuncin gasar wasannin daliban jami’o’i ta duniya, inda na ga yadda kasar ta shirya tsaf domin takaita abubuwan da ka iya gurbata muhalli. Misali, yadda motocin sufurin yayin gasar ke amfani da makamashi mai tsafta da yadda aka samar da na’urorin samar da lantarki daga makamashi mai tsafta da sauransu.
Haka zalika, su ma jama’ar kasar Sin suna kokarin rungumar hanyar da ta dace na rage fitar da hayaki mai guba. Misali, bayanai sun nuna cewa, a rabin farkon bana kadai, an yi wa kimanin sabbin motoci miliyan 3.13 masu amfani da sabon makamashi rejista, adadin da ya karu da kaso 41.6 a kan na bara, wanda kuma ya kai matsayin koli.
Dama dai Amurka ce ke jan kafa kan batun sauyin yanayi inda take kokarin mayar da hannu agogo baya game da yarjejeniyoyin da aka cimma da kuma kin cika alkawurranta. Fatan ita ce yadda manyan jami’anta ke zarya a kasar Sin, ya kasance ta cika alkawuranta ta kuma dauki darasi daga kasar Sin, tare da hada hannu da ita wajen tabbatar da kafuwar duniya mai aminci da tsaro makoma ta bai daya ga daukacin bil adama.