logo

HAUSA

Sin ta bukaci kasashen duniya su hada hannu wajen kare yanayin Ukraine daga kara tabarbarewa

2023-07-18 13:58:52 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce tun bayan barkewar rikicin Ukraine, yanayin ya ci gaba da tsawaita, da fadada da kara sarkakiya, yana mai cewa, ya kamata kasashen duniya su hada hannu wajen kare yanayin daga kara tabarbarewa.

Geng Shuang ya bayyana haka ne ga taron Kwamitin Sulhu kan batun Ukraine a jiya, inda ya kara da cewa, ya kamata a cimma dakatar da bude wuta da kawo karshen rikicin nan bada jimawa ba, da kuma warware batun a siyasance.

Ya ce a watan Fabrerun bana, Sin ta gabatar da wani daftari mai taken “Matsayar Kasar Sin kan Warware Rikicin Ukraine a Siyasance”. Kuma bisa hakan ne Sin din za ta ci gaba da hada hannu da kasashen duniya wajen kokarin warware batun a siyasance, ba tare da yin kasa a gwiwa ba. (Fa’iza Mustapha)