logo

HAUSA

A karon farko an samu wani nau’in annobar cutar dabbobi a arewa ta tsakiyar Najeriya

2023-07-18 09:20:27 CMG Hausa

Ma’aikatar noma da albarkar kasa ta tarayyar Najeriya ta sanar jiya Litinin 17 ga wata cewa, an samu bullar cutar dabbobi ta Anthrax dake saurin yaduwa tare da halaka dabobi cikin hanzari a wani gidan gona dake garin Suleja na jihar Niger dake arewa ta tsakiyar Najeriya.

Bayanin haka na kunshe ne cikin wata sanarwa daga babban likitan dabbobi na kasa Dr. Columba Vakuru, bayan ya sanar da bullar annobar ga ma’aikatar gonar. Ya ce, an fara gano cutar ne tun a ranar 14 ga wata bayan wani bincike da aka gudanar a jikin wasu shanu da suka nuna alamar cutar.

Daga tarayar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Daga cikin alamonin cutar dai sun hada da zazzabi mai tsanani da rashin fitar da numfashi kamar yadda ya kamata, da tari da kuma ciwon kirji, da fitar jinni ta ido da kuma hanci.

Dr. Colunba ya ce, tun bayan tabbatar da cutar, gwamnatin tarayyar tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihar Niger suka fara daukar matakan gaggawa domin dakile yaduwarta, ta hanyar killace gonar da shanun suke .

Ko da yake ya ce ba wai shanu ne kawai a gidan gonar ba, gidan gonar ya kunshi garken awaki da tumakai wanda dukkanninsu cutar tana tasiri a kan su.

Babban likitan dabbobin dake ma’aikatar gona ta tarayyar Najeriya ya ci gaba da cewa, hadin gwiwar jami’an lafiya na tarayyar da na jihar ta Niger sun dauki nau’in wasu daga cikin dabbobin da annobar ta shafa domin gudanar da gwaje-gwajen kimiya a kansu, ta yadda za a kara tsananta bincike tare da kokarin gano magungunan da za su yi saurin maganin cutar.

Ya ce wannan shi ne karon farko da aka samu irin wannan nau’in cutar a Najeriya, duk da cewa a ’yan makwannin da suka gabata an samu rahoton cutar a yankunan dake arewacin Ghana wadanda ke da makwaftaka da kasashen Togo da Burkina Fasso.

A sabo da haka ma’akatar gonar ta tarayyar Najeriya ke kira ga masu kiwon dabbobi a duk inda suke a kasar da su kara lura sosai tare da kai rahoton duk wani nau’i na rashin lafiyar dabbobin su ko kuma mutuwar dabbobin, sannan kuma an ja hankalin jama’a da su rinka nesanta kansu daga mushen dabba ta hanyar ci ko cinikin wani sashe na jikin su domin su kansu ’yan adam cutar na iya shafar su sosai.

Ha`ila yau ma’akatar gonar ta tarayyar Najeriya ta gargadi al’ummar kasar dasu rinka taka-tsantsan wajen sayen dabobi irin su Saniya, Akuya, Raguna, Rakuma, Aladu daga garuruwan da suke kan iyakokin Najeriya da kasashen Benin, da Chadi, da Niger, da Ghana, da ma sauran kasashen da suke yammacin Afrika.

Bincike ya nuna cewa dabbobin na daukar wannan cuta ne a kasa, ko jikin itatuwa ko kuma fatu na dabbobin da suka kamu da cutar. (Garba Abdullahi Bagwai)