logo

HAUSA

Shugaban Jam'iyya Mai Mulki a Najeriya da Sakataren Sun Yi Murabus

2023-07-18 10:31:19 CMG Hausa

A jiya Litinin ne wani babban jami’in jam’iyyar ya bayyana cewa, Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, da sakataren jam’iyyar na kasa Iyiola Omisore sun yi murabus. 

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa Abubakar Kyari, ya shaidawa manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya cewa, Adamu da Omisore ba sa cikin shugabannin jam'iyyar APC a yanzu, inda ya kara da cewa bisa kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC, yanzu shi ne shugaban jam’iyyar na kasa mai rikon kwarya, yayin da mataimakin sakatare na kasa Festus Fuanter zai zama sakataren rikon kwarya. (Yahaya)