logo

HAUSA

Ministan cikin gidan Nijar ya kai ziyara aiki a Ouro Gueladjo domin ganawa da al’umomin da suka kaura daga muhallinsu

2023-07-18 09:22:36 CMG Hausa

Ministan cikin gida, Hamadou Adamou Souley ya kai wani rangadi a cikin karamar hukumar karkarar Ouro Gueladjo cikin jahar Say a wannan mako domin ganewa idonsa halin da mutanen da suka kaura daga kauyukansu ta dalilin hare haren ’yan tadda a yankin Tillabery. 

Daga birnin Yamai, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Makasudin wannan rangadi shi ne na sannin yanayin zaman rayuwar al’umomin da suka tsere daga yankunansu dalilin hare-haren kungiyoyin ta’addanci masu makamai. Ruwan sama da aka samu kamar da bakin kwarya a ’yan kwanakin baya bayan nan sun sanya ratsa tafkin Goroubi da wahala sosai har ma wajen tsaron kauyukan da ke gabar dama ta tafkin shi ma da matukar wuya. Hakika, mazaunan kusan kauyuka 14 na Ouro Gueladjo suka tsara tafkin Goroubi domin su samu mafaka a babban birnin Ouro Gueladjo, Torodi da Yamai.

A cewar ministan cikin gida, manyan ruwan da aka samu sun kawo cikas ga jami’an tsaro domin zuwa wasu yankuna. Tare tunbatsar ruwa, akwai wuya ga jami’an FDS da ke koda yaushe a kewayen Ouro Gueladjo su samu zarafin ruwa domin ba da kariya ga al’umomin da ke gabar daman Goroubi. ’Yan ta’adda sun jira wannan lokaci domin farma al’umomi da korarsu daga ciklin kauyukansu. Nan take muka samu labari, in ji ministan cikin gida. Mun dauki matakai ta fuskar tsaro nan da nan. Akwai sojoji da aka zuba ko’ina, kuma suna nan suna ayyukan kakkaba cikin wannan yankin baki daya. Muna jiran karshen ayyukan soja har sai an kawar da miyagun mutanen daga yankin domin bada umurni ga al’umomin su dawo cikin kauyukansu in ji ministan cikin gida. 

Inda ya kara da cewa, mun zo domin ganawa da wadannan al’umomi domin tabbatar musu da niyyar gwamnati ta kawo kwanciyar hankali da tsaro. Haka kuma, ministan tsaron ya yaba da kokarin mutanen kauyukan da suka karbi bakuncinsu da kuma juriyar wadannan mutane da suka baro wurarensu, mun lura cewa wani taimakon juna ya bunkasa. Wannan kuma, tare da taimakon magajin gari, sarakunan gargajiya, domin wadannan baki an tarbe su kuma an tsugunnar da su cikin makarantun gwamnati da kuma gidan jama’a, duk da yawan nasu, babu wanda ya nuna damuwa bisa ga tarbon da aka musu. Ina jinjinawa al’ummar Ouro Gueladjo bisa ga zumuncin da ta nunawa wadannan mutane.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.