logo

HAUSA

Tasirin raba gari da Sin zai wuce batun cinikayya, in ji jaridar “Morning Post”

2023-07-18 14:16:55 CMG Hausa

Aniyar Amurka ta raba gari da kasar Sin, ko abun da Amurkar ke kira kaucewa hadarin kasar Sin, manufofi ne da ka iya yin mummunan tasiri ga karin sassa, baya ga batun kasuwanci. Hakan na kunshe cikin wata makalar marubuci Anthony Rowley, wadda jaridar “Morning Post” ta yankin Hong Kong ta wallafa.

Mista Rowley, wanda kwararre ne a fannin nazarin tattalin arziki da hada-hadar kudi a yankin Asiya, ya ce irin wadannan matakai idan suka dore, su na iya haifar da matsalar kariyar cinikayya, da kebe kai, da gurgunta bunkasar cudanyar sassa daban daban. Kaza lika hakan na iya gurbata yanayin hadin gwiwar bangarorin kasa da kasa, lamarin da ka iya kunna wutar kiyayya.

Rowley ya kara da cewa, wadannan manufofi masu haifar da wariya da Amurka ke aiwatarwa, ko kadan ba su dace da matsayin jagoranci na gaskiya ba. (Saminu Alhassan)