logo

HAUSA

Babban bankin Masar ya sanya hannu kan takardun fahimtar juna biyu domin raya sha’anin ayyukan cibiyoyin hada hadar kudi

2023-07-18 13:54:21 CMG Hausa

Babban bankin kasar Masar, ya sanya hannu kan takardun fahimtar juna guda biyu, tare da babban bankin Najeriya CBN, da kuma cibiyar harkokin banki da hada hadar kudi ta Landan, domin raya ayyukan cibiyoyin hada hadar kudi.

Kafar watsa labarai ta Ahram dake Masar ce ta tabbatar da cimma wannan mataki, inda ta ce babban bankin Masar ko CBE, ya sanya hannu kan takardar fahimtar juna da babban bankin Najeriya, don inganta musaya a fannin amfani da fasahohin yanar gizo na zamani a ayyukan banki, da kirkire-kirkire, da biyan kudade ta yanar gizo, da hade damar cinikayya ta yanar gizo.

A daya bangaren kuma, CBE ya sanya hannu kan takardar fahimtar juna da cibiyar harkokin banki da hada hadar kudi ta Landan, domin samar da horon sanin makamar aiki a fannoni daban daban, da tarukan karawa juna sani, da kwasa-kwasai a fannin jagorancin bunkasa ayyukan banki ta amfani da fasahohin zamani.

An dai rattaba hannu kan takardun fahimtar junan guda 2 ne a jiya Litinin a kasar Masar, a gefen taron nazarin dabarun raya sha’anin ayyukan cibiyoyin hada hadar kudi na yankin arewacin Afirka na shekarar 2023.  (Saminu Alhassan)