logo

HAUSA

CDC ta Afirka ta yi alƙawarin gaggauta mayar da martani ga barkewar cututtuka

2023-07-17 10:44:45 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne wani babban jami'in hukumar yaki da cututtuka ta Afirka (CDC Afrika) ya ce, cibiyar ta ba da fifiko wajen tunkarar cututtuka masu saurin yaduwa cikin gaggawa a matsayin yunkurin inganta tsarin kiwon lafiya a nahiyar.

Jean Kaseya, babban darektan cibiyar yaki da cututtuka ta CDC ta Afirka, ya ce daukar matakan da suka dace, da isassun kayan aiki, da gudanar da ayyuka cikin lokaci da kuma tsarin da ya dace, game da lalurorin kiwon lafiyar jama'a na nahiyar ciki har da barkewar cututtuka ya zama wajibi.

Da yake magana a gefen taron koli na tsakiyar shekara na kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, Kaseya ya ce, bisa darussan da aka koya daga cutar COVID-19, CDC ta Afirka tana taimakawa kasashe su samar da tsare-tsare na gaggawa na kiyaye barkewar cututtuka tare da kawar da asarar rayuka da kuma rage nauyi a cibiyoyin kiwon lafiyar jama'a.

Kazalika, Kaseya ya ce, cibiyar CDC ta Afirka tana kuma hada gwiwa da kungiyoyin kasashen yankin don karfafa bincike, da bayar da rahoto da sa ido kan cututtuka masu yaduwa kamar Ebola, cutar Marburg, zazzabin Rift Valley da zazzabin cizon sauro.

Ya kara da cewa, inganta samar da alluran rigakafi na cikin gida, da magunguna da na'urorin kariya za su kuma karfafa kasashen Afirka wajen magance matsalolin kiwon lafiya. (Yahaya)