logo

HAUSA

Shugabannin Afirka sun yi kira da a yi garambawul ga tsarin manyan cibiyoyin kudi na duniya

2023-07-17 11:43:07 CMG Hausa

 

Shugabannin kasashen nahiyar Afirka, sun yi kira da a yi garambawul ga tsarin hada hadar kudade na manyan cibiyoyin kudi na duniya, da kuma dunkule sassan tattalin arziki, yayin taron su na tsakiyar shekara da aka bude a jiya Lahadi.

Da take tsokaci yayin taron, mataimakiyar sakatare janar na MDD Amina Mohamed, ta ce duniya na ci gaba da fuskantar matsaloli daban daban, wadanda ke yin tasiri ga zamantakewa, da tattalin arzikin al’ummu daban daban sakamakon annobar COVID-19 da aka sha fama da ita.

Jami’ar ta kara da cewa, nahiyar Afirka ce ta fi fama da tasirin wannan yanayi, sakamakon rashin cika alkawuran samar da kudaden yaki da sauyin yanayi, daga cibiyoyin hada hadar kudade na duniya, da karancin tallafin jin kai dake kara haifar da tsaiko ga yunkurin kasashen Afirka, da jagororin su, na aiwatar da ajandar nahiyar nan da shekarar 2063.

Amina Mohamed, ta ce MDD na tare da shugabannin Afirka, a kiraye kirayen su na samar da karin albarkatun bunkasa tattalin arzikin su, karkashin lemar asusun ba da lamuni na IMF, wanda akasarin shugabannin nahiyar ke sukar lamirin manufofin sa.

A nasa jawabin, shugaban kasar Kenya William Ruto, wanda ya goyi bayan sauran jagorori mahalarta taron, wajen yin kira da a aiwatar da sauye-sauye ga bankin duniya da asusun IMF, ya ce nahiyar Afirka na fuskantar rashin adalci tsakanin kasashen duniya a tsarin karba da biyan bashi, matakin da ke sanya su biya a kalla ninki 8 na bashin da ake binsu, sama da sauran kasashe masu wadata.  (Saminu Alhassan)