logo

HAUSA

Ziyarar shugaban Aljeriya a kasar Sin za ta karfafa dangantakar kasashen biyu

2023-07-17 11:49:29 CMG Hausa

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune na ziyarar aiki a kasar Sin daga yau Litinin 17 zuwa 21 ga wata, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa.

Da yake tsokaci don gane da ziyarar, shugaban kungiyar raya abota tsakanin Sin da Aljeriya, Isma’il Dabash, ya ce wannan ne karo na farko da shugaban na Aljeriya ya ziyarci kasar Sin tun bayan hawa karagar mulkin kasar, kuma ya yi imanin cewa, ziyarar za ta kara kyautata dangantakar abota dake tsakanin kasashen biyu.

A cewar Isma’il Dabash, kasar Sin ta taimakawa Aljeriya a shekarun 1950, lokacin da kasar ke fafutukar neman ‘yanci. Yana mai cewa, Sin ce kasa ta farko da ba ta Larabawa ba, da ta amince da kasar Aljeriya. Haka kuma Aljeriya a nata bangare, ta taimakawa Sin matuka, wajen dawo da halaltacciyar kujerarta a MDD. Ya ce shaidu sun nuna cewa Aljeriya da Sin sun kasance masu taimakon juna kuma aminai dake hadin gwiwa.

Bugu da kari, Isma’il Dabash ya ce Aljeriya ta shiga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya a shekarar 2018, kuma kasashen biyu sun rattaba hannu kan shawarar a shekarar 2022. Ya jaddada cewa, shigar Aljeriya cikin shawarar ba karfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakaninta da Sin kadai zai yi ba, har ma da karawa tattalin arzikinta kuzarin bunkasuwa. (Fa’iza Mustapha)