logo

HAUSA

80% daga cikin ’yan matan da aka ceto daga hannun ’yan boko haram suna karatu a manyan makarantun kasar Najeriya

2023-07-17 09:22:03 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa ’yan mata 80 daga cikin adadin ’yan matan da dakarun tsaron kasar suka ceto daga hannun ’yan kungiyar Boko Haram suna gudanar da karatun su a manyan makarantun kasar daban daban. 

Babbar sakatariya a ma’aikatar ilimi ta tarayyar Najeriya Mrs Monilola Udoh ce ta tabbatar da hakan  a karshen makon jiya yayin wani taro da wakilan kwamitin tsaro na majalissar dinkin duniya da suke bibiyar rayuwar kananan yara bayan hare haren ’yan ta’adda a kasashe, kwamitin dake karkashin jagorancin Christian Monduate.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Babbar sakatariyar ma’aikatar ilimin ta tarayayr Najeriya ta ce tun daga watan Maris na shekara ta 2017, gwamnatin tarayya ta hannun ma’akatar lura da al’amuran mata suka kulla aikin hadin gwiwa da wasu kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka hada da wakilan hukumomin majalissar dinkin duniya kamar hukumar UNICEF da hukumar lura da mata da kananan yara  na majalissar dinkin  duniya wajen mayar da ’yan matan Chibok da aka ceto makaranta. 

Mrs Monilola ta ci gaba da cewa duk an sami nasarar hakan ne ta hannun ma’aikatar ilimin ta tarayya da kuma kwamitin musamman na shugaban kasa a kan asusun tallafawa wadanda hare-haren ’yan Boko Haram ya ritsa da su a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Babbar sakatariya a ma’aikatar ilimin ta tarayyar Najeriya, har’ila yau ta ce ma’aikatar tare da hadin gwiwa da kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa suna kokari wajen wayar da kai game da illolin dake tattare da auren dole wanda ’yan ta’addan Boko Haram a baya suka yi ta aikatawa a shiyyar arewa masu gabashin kasar.

Haka kuma an ceto mata da dama da suka shiga kangin talauci sakamakon rashin zaman lafiya, ta hanyar samar masu da rance mara ruwa da kuma kayayyakin sana’o’i daban daban, wanda wannan ya taimaka musu sosai wajen lura da dawainiyar ’ya’yan su da suke a matsayin marayu.

Daga karshe a nata jawabin, jagorar ayarin majalissar dinkin duniyar Mrs Christian Monduate ta ce sun zo Najeriya ne domin bibiya tare da nazartar yadda ake lura da kananan yaran da dakarun tsaron kasar suka ceto daga bala’in hare-haren ’yan ta’adda, inda ta yaba bisa irin tsare-tsaren da kasar ke bi a halin yanzu. (Garba Abdullahi Bagwai)