Sin tana kiyaye matsayinta na zama ginshikin ci gaban duniya
2023-07-17 21:31:37 CMG Hausa
An fara aikin samar da batir na BMW na zamani na 6 da jimlar jarin Yuan biliyan 10 a birnin Shenyang, kamfanin samar da alluran rigakafi na kasar Amurka, mai suna Moderna ya sanya hannu kan yarjejeniyar saka hannun jari a kasar Sin, inda ake shirin gudanar da bincike, kera da sayar da magungunan mRNA a kasar Sin. Tun wannan shekarar jarin waje da ake zubawa a kasar Sin ya karu.
An kara tabbatar da amincewarsu a watanni 6 na farkon shekarar 2023 a cikin bayanan tattalin arzikin kasa da gwamnatin kasar Sin ta fitar Litinin din nan. Bisa kiddigar farko, yawan GDP na kasar Sin a watanni 6 na farkon bana, ya kai yuan biliyan 59303.4, adadin da ya karu da kashi 5.5 cikin 100 a duk shekara. Wannan ci gaban ya fi na manyan kasashen da suka ci gaba a duniya sauri, kuma kasar Sin na ci gaba da zama injin din ci gaban duniya.
Game da jarin waje, wannan yana nufin babbar damar dake akwai a kasuwar kasar Sin. Alkaluman kididdigar da hukumar kula da kudaden waje ta kasar Sin ta fitar, na nuna cewa, yawan ribar da aka samu daga jarin waje da aka zuba a kasar Sin a cikin shekaru biyar da suka gabata, ya kai kashi 9.1 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 3 cikin 100 da aka samu a kasashen Turai da Amurka. (Ibrahim)