logo

HAUSA

Masani Habasha ya yi karin haske kan zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka

2023-07-16 15:16:58 CMG Hausa

An kaddamar da wani sabon littafi jiya Asabar mai taken "Hadin gwiwar Afirka da Sin: Nazari kan Habasha" wanda ke nuna dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka daban-daban, mai cike da tarihi, musamman kan alakar dake tsakanin kasashen Sin da Habasha.

Littafin mai babi 7, sun yi karin haske kan fannonin da suka hada da manufar kasar Sin game da nahiyar Afirka, da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Habasha da Sin, da hadin gwiwar siyasa tsakanin Afirka da Sin.

Bugu da kari, littafin ya yi nazari kan nasarorin da aka cimma a dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka a lokacin annobar COVID-19, da kuma nazari kan alakar dake tsakanin Sin da Afirka a karni na 21.

An kaddamar da littafin ne a gaban manyan jami'an gwamnatin Habasha, da jami'an diflomasiyyar kasar Sin dake kasar Habasha, da shugabanni da wakilan cibiyoyin nazari daban-daban, gami da masana da sauran su.

Marubucin littafin, Melaku Mulualem, wanda babban jami'i ne mai bincike kan huldar kasa da kasa da harkokin diflomasiyya a cibiyar kula da dabarun kasar Habasha, ya bayyana cewa, kasashen Sin da Afirka sun raya dangantaka mai dinbin tarihi cikin wadannan shekaru, wanda kuma ke kara habaka a 'yan shekarun nan.

Marubucin ya kuma tuna abubuwan da ya koya a jami'ar harkokin waje ta kasar Sin, a matsayin abin da ya ba shi kwarin gwiwa wajen rubuta littafin, wanda ya ce, ya nuna hakikanin hadin gwiwar samun nasara tare, a tsakanin kasashen Sin da Habasha. (Ibrahim)