logo

HAUSA

An bukaci da a sake dawo da shirin dashen itatuwa da ake yi a duk shekara a tarayyar Najeriya domin maganin hamada

2023-07-16 15:24:53 CMG HAUSA

 

Sarkin Kano dake arewacin Najeriya Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira da a sake maido da shirn dashen itatuwa na kasa da aka saba gudanarwa a duk shekara domin maganin kwararowar hamada da kare muhalli.

Yayi kiran ne a karshen mako a fadar sa lokacin daya karbi bakuncin darakta janar na hukumar kare zaizayar kasa da sauyin yanayi na tarayyar Najeriya Dr. Yusuf Maina Bukar, yace wajibi ne jama’a su rungumi halayyar dasa bishiyoyi a muhallan su.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.