logo

HAUSA

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Yi Kokarin Kare Zaman Lafiyar Yankin Gabashin Asiya

2023-07-15 17:08:42 CMG Hausa

Babban jami’in diflomasiyya na kasar Sin Wang Yi, ya yi kira yayin taron kasashen yankin gabashin Asiya a jiya cewa, ya kamata a yi kokarin kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, bisa la’akari da manyan sauye-sauyen dake akwai a yanayin yankuna da ma duniya.

Da yake halartar taro na 13 na ministocin harkokin wajen kasashen gabashin Asiya, Wang Yi, wanda shi ne daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiya na JKS, ya ce taron gabashin Asiya wani dandali ne na hadin gwiwa dake da wakilici daga dukkan bangarori, kuma yana da muhimmin tasiri kan yankin Asiya da tekun Fasifik.

Ya ce kasar Sin na son gabatar da wasu shawarwari 3 da suka hada da, na farko, mara baya ga kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN da shimfida kwakkwaran tubalin wanzar da zaman lafiya. Na biyu, hada hannu wajen gina yankin zuwa wata cibiyar ci gaba da inganta ci gaba na bai daya. Na uku, mara baya ga huldar bangarori daban-daba da inganta kyakkyawar mu’amala.

Har ila yau a jiyan, Wang Yi ya gabatar da wasu shawarwari 3 na kare zaman lafiya da tsaro a yankin Asiya da tekun Fasifik, yayin taron ministocin harkokin waje na dandalin tattaunawar yankin kungiyar ASEAN.

Shawara ta farko ita ce, nacewa bude kofa da tafiya tare, da inganta tsaro na bai daya. Shawara ta biyu ita ce kare dokoki da ka’idojin yankin, da inganta tsaro na gama gari. Ta uku kuwa ita ce, zurfafa hadin gwiwa da tabbatar da tsaro cikin hadin gwiwa.  (Fa’iza Mustapha)