logo

HAUSA

Majalissar dokokin Najeriya ta kawo shawarar samar da karin jami’an tsaro a kauyukan dake kan iyakar Najeriya da kasashe makwabta

2023-07-15 16:36:38 CMG Hausa

Majalissar wakilan tarayyar Najeriya ta gabatar da kudurin dake neman karin jami’an tsaro a kauyukan jihar Sakkwato wadanda ke kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar.

Samar da karin jami’an tsaro zai kawo karshen yawan karbar kudin fansa da masu ikirarin jihadi ke yawan yi ga al’ummomin dake zaune a irin wadannan garuruwa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Batun karbar kudin fansa daga wurin wasu al’umomin dake wasu yankuna a arewacin Najeriya har yanzu yana ci gaba da gudana duk kuwa da kokarin da hukumomin tsaron kasar ke yi.

Jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara a yanzu haka irin wannan ta’addanci na haifar da zaman dar dar ga wasu daga cikin al’umomin dake zaune a wasu garuruwan dake daf da iyakoki.

Da yake gabatar da kudurin a zaman majalissar Hon. Sani Yakubu  wanda yake wakiltar mazabar Tangaza da Gudu a jihar Sakkwato a zauren majalissar ta tarayya ya ce, sau tari masu ikirarin jihadi da suka fito daga kasashen Jamhuriyar Benin da Mali da kuma Libya su ne suke tsallakowa zuwa irin wadanann garuruwa suna sace jama’a tare da neman kudin fansa.

Dan Majalissar ya ce ’yan ta’addan na amfani da dazukan Tsauna da kuma na Kuyan Bana wanda dukkanninsu sun ratsa ta cikin jamhuriyyar Nijar wajen aikata wannan aika-aika.

A cewar dan majalisar yanzu kungiyoyin ’yan ta’adda dake yankin sun hade kan su, inda suka yi barazanar hana manoma gudanar da noma da kiwo wadanda irin wannan sana’a suka dogara.

A farkon makon da muke bankwana da shi ne, shugaban rundunar sojin kasa na Najeiya Manjo Janar Toereed Lagbaja ya tabbatar da cewa, dakarun sojin Najeriya dai sun kara daura damarar yakar duk wani dan ta’adda dake kasar ba ma kawai a jihohin arewacin Najeriya ba.

A ’yan watannin nan dai an dan samu saukin hare-haren ’yan ta’adda a wasu sassan Najeriya musamman ma a shiyyar arewa maso gabas da kuma shiyyar arewa ta yamma. (Garba Abdullahi Bagwai)