logo

HAUSA

AU Za Ta Aiwatar Da Dabarun Shawo Kan Matsalar Yunwa A Afrika

2023-07-15 16:26:32 CMG Hausa

Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), za ta aiwatar da wani shirin cimma burin ganin wadatar abinci a nahiyar Afrika, domin shawo kan matsalolin yunwa da na tamowa da matsalar yanayi ta haifar a nahiyar.

Kwamishinan AU mai kula da fannonin aikin gona da raya karkara, da tattalin arzikin teku, da muhalli mai dorewa, Josefa Sacko ya ce daga cikin mutane miliyan 828 da hukumar samar da abinci da raya aikin gona ta MDD (FAO) ta lissafa a matsayin masu fama da matsalar abinci a duniya, miliyan 278 na nahiyar Afrika.

Ya ce domin tunkarar matsalar karancin abinci a Afrika, AU ta amince da daukar kwararan matakan bunkasa samun amfanin gona ta hanyar kara yawan jari a bangaren aikin gona.

Ya kara da cewa, kasashe mambobin AU ne za su aiwatar da matakan da kuma abokan hulda na kasa da kasa, ciki har da kasar Sin, da suka samar da tallafin kudi domin tallafawa bunkasa aiwatar da dabarun dake da burin bukasa wadatar abinci a nahiyar.  (Fa’iza Mustapha)