logo

HAUSA

Fiye de mutane 10,800 suka gujewa tashe tashen hankali tun farkon watan Julin shekarar 2023 a kudu maso yammacin Nijar

2023-07-14 13:49:58 CMG Hausa

Fiye da mutane 10,800 daga cikinsu mata da yara kanana daga goman kauyuka na kudu maso yammacin Nijar, kusa da Burkina Faso, suka bar gidajensu tun farkon watan Yulin shekarar bana, dalilin tashe-tashen hankalin mutane dauke da makamai.

Daga birnin Yamai, abokin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

A cewar hukumomin jahar Say, iyalai 1570 da suka cimma fiye da mutane 10,800 na kauyuka guda 9 na karamar hukumar Ouro Gueladjo aka tilasta ma barin gidajensu a tsawon kwanaki 10 na farkon watan Yuli.

Wadannan mutane sun tsere wa tashe-tashen hankali na kungiyoyi masu makamai da ba na gwamnati ba da ke cikin yankin Tillabery da kuma cikin yankin iyakoki uku da suka hada kasashen Nijar, Burkina Faso da Mali, a cewar wata sanarwar ma’aikatar harkokin jin kai ta majalisar dinkin duniya OCHA da ke birnin Yamai.

Fiye da mutane 8430 suka samu mafaka a Ouro Gueladjo, yayin da fiye da mutane 2140 suka tsere zuwa Torodi, yayin da kuma mutane 215 suka shigo birnin Yamai, a cewar wata kididdiga ta OCHA da hukumomin kasa.

A cewar OCHA, matsalar jin kai na tsanani a garin Ouro Gueladjo inda wadannan mutane suka tsere suka bukatar matsuguni, abinci da kula da lafiyarsu da kuma ruwan sha masu tsafta.

Tuni gwamnatin Nijar ta fara rarraba abinci na kusan ton 85 tare da kara karfafa matakan tsaro a wadannan yankuna da ke fama da hare-haren ta’addanci.

Sai dai wadannan kungiyoyin ta’addanci sun kara tsananta da aiwatar da sabbin salon kai hare hare da suka hada da kisa, satar mutane, aza nakiyoyi da kuma ba da umurni ga mutane da su bar gidajensu musamman ma a yankin iyaka da Burkina Faso.

A cewar MDD, yankin Tillabery na karbar fiye da mutane dubu 150 da suke hijira a cikin gida. (Mamane Ada)