logo

HAUSA

Rundunar sojojin gwamnatin Sudan ta kuduri aniyar aiki tare da dukkanin sassa don shawo kan tashin hankalin dake addabar kasar

2023-07-14 10:18:22 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sudan, ta sha alwashin hada kai da dukkanin sassa wajen kawo karshen tashin hankalin dake addabar kasar. Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da majalissar kolin kasar ta fitar, wadda ke cewa, rundunar sojojin gwamnatin kasar ta shirya dakatar da daukar matakan soji nan take, idan har dakarun sa kai na kasar sun amince su daina kaiwa fararen hula, da unguwanni, da gine ginen gwamnati hare hare.

Kaza lika, sanarwar ta ce sojojin gwamnati sun yi maraba da sakamakon taron da kasashe makwaftan kasar suka gudanar a birnin Alkahiran kasar Masar.

A jiya Alhamis ne dai aka gudanar da taron na Alkahira, da nufin tattauna dabarun kawo karshen yakin da ke daidaita kasar Sudan. Kuma sanarwar bayan taron ta ayyana cewa, kasashe mahalartansa sun yi watsi da batun shigar kasashen ketare cikin rikicin Sudan, suna masu kira da a gaggauta gudanar da cikakkiyar tattaunawa tsakanin sassa biyu dake dauki ba dadi da juna a kasar.

Har ila yau, taron ya amince da kafa wani kwamitin ministoci, wanda zai tsara, tare da aiwatar da shirin da zai kai ga shawo kan yakin Sudan, kuma an amince kwamitin ya gudanar da zaman sa na farko a kasar Chadi. (Saminu Alhassan)