logo

HAUSA

An yi bikin sanya hannu kan yarjejeniyar mika asibitin zumunta na Sin da Equatorial Guinea

2023-07-14 13:26:58 CMG Hausa

An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar mika asibitin zumunta na Sin da Equatorial Guinea wanda kasar Sin ta tallafa wajen ginawa. An gudanar da bikin ne a jiya Alhamis, a birnin Bata na lardin Litoral dake Equatorial Guinea.

Da yake tsokaci yayin bikin, babban jami’i a ofishin jakadancin Sin dake kasar Chen Yong, ya ce sanya hannu kan yarjejeniyar mika asibitin ga mahukuntan Equatorial Guinea, shi ne matakin farko na kaiwa ga bude shi. Ya ce ya yi imanin cewa, bisa hadin gwiwar kasashen biyu, za a kai ga bude wannan asibiti nan ba da jimawa ba, wanda hakan zai amfani al’ummun Equatorial Guinea.  (Saminu Alhassan)