logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen kasashen Afirka sun sabunta kudurin dunkulewar ajandar ci gaban nahiyar

2023-07-14 11:14:49 CMG Hausa

Ministocin harkokin wajen kasashen Afirka sun bayyana cewa, farfado da tattalin arzikin kasashen nahiyar ta hanyar yin cinikayya mara shinge, da inganta matakan samar da kayayyaki, da samar da guraben ayyukan yi, za su taimaka matuka wajen magance matsalar fatara, da zaman rashin tabbas da rashin aikin yi ga matasa.

A jawaban da suka gabatar yayin wani taron tattaunawa da kungiyar tarayyar Afrika AU ta kira a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, sun jaddada cewa, idan har nahiyar na son aiwatar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki, to, wajibi ne ta ba da fifiko wajen zirga-zirgar kayayyaki da kwararrun ma'aikata.

Kasar Kenya na daukar bakuncin taro karo na biyar da ake gudanarwa a tsakiyar ko wace shekara, wanda kungiyar AU da na shiyya-shiyya suka kira daga jiya Alhamis zuwa ranar Lahadi, mai taken "hanzarta aiwatar da yarjejeniyar cinikayya mara shinge ta Afirka (AfCFTA)".

Ma'aikatar harkokin waje da mazauna ketare ta Kenya ta bayyana cewa, shugabannin kasashe da gwamnatoci 14, da ministocin harkokin waje daga kasashe mambobin kungiyar AU guda 51, da wakilai dubu 1 da 500, ne ake sa ran za su halarci taron.(Ibrahim)