logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin daukar managartan matakan inganta muhalli

2023-07-14 11:13:46 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha alwashin daukar managartan matakai da za su tabbatar da ingantaccen muhalli.

Babban sakatare a ma’aikatar muhalli ta kasa Alhaji Ibrahim Idris ne ya tabbatar da hakan jiya Alhamis 13 ga wata yayin bikin ranar tsaftar muhalli na kasa na 2023. Ya ce, sharar da Najeriya ke samarwa a duk shekara wadda ta kunshi robobi da sauran tarkace ya kai ton miliyan 1.5 kuma 10% kawai ake iya sake sarrafawa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Taken ranar tsaftar muhallin na bana dai shi ne “dorewar kula da shara tare da dakatar da zubar da sharar a ko’ina”.

Alhaji Ibrahim Idris ya ce, rashin kyawun muhalli na daya daga cikin manyan dalilan dake haifar da yaduwar cuttuttuka daban daban a kasashe masu tasowa ciki har da Najeriya.

Babban sakataren ma’aikatar muhallin ta tarayyar Najeriya ya ce batun tsaftar muhalli ba shi da wani lokaci tsayayye, harkar lura da muhalli batu ne na yau da kullum saboda shi ne jigon rayuwar kowanne bil’adama.

Jihar Kano na daya daga cikin manyan biranen Najeriya da suke samar da tarin shara, saboda yawan hada-hadar jama’a.

Kamar da yadda binicke ya tabbatar a kowacce rana a cikin birnin Kano, ana samun sharar da ta kai tan 3085.

Alhaji Ahmadu Haruna Dan Zago shi ne manajan daraktan hukumar kwashe shara ta jihar Kano, ya tabbatar wa wakilin CRI cewa tun kafin ranar ta jiya Alhamis hukumar ta dukufa wajen tabbatar da tsaftar muhalli a cikin kwaryar birnin Kano.

“A jiya mun kaddamar da feshin maganin gidan sauro da kwari daban daban kuma mun yi hayaki na magani a tsakanin karfe 7-8 na daren Laraba, inda muka yi a wurare da dama kamar asibitoci wadanda suka hada da asibitin Sir Sunusi, sa asibitin Jakara da asibitin Marmara da asibitin Waziri Gidado, kuma batun shara yanzu kowanne titi muna bi muna kwashewa.”

Ita dai wannan rana ta tsaftar muhalli ta kasa ana gudanar da ita ne a duk ranar 28 ga watan Yuni a tarayyar Najeriya, to amma sabo da yanayi na bikin babbar salla, ya sanya gwamnati ta mayar da ita zuwa jiya Alhamis 13 ga watan Yuli. (Garba Abdullahi Bagwai)