logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da dokar ta baci kan samar da isasshen abinci

2023-07-14 15:25:47 CMG Hausa

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta baci a fannin samar da isasshen abinci, da nufin aiwatar da dukkanin matakan da suka wajaba, na shawo kan tasirin hauhawar farashin abinci dake takura rayuwar al’ummar Najeriya.

Alkaluman kididdiga na hukumar NBS, sun nuna daidaitar karuwar farashin kayayyakin masarufi a kasar tun daga farkon shekarar 2021 da ta gabata. A watan Mayun da ya shude kuma, alkaluman awon farashin kayayyaki a kasar ya karu da kaso 22.4 bisa dari a shekara, inda farashin kayayyakin abinci ya karu da kaso 24.8 bisa dari a shekara. (Saminu Alhassan)