logo

HAUSA

Sin da ASEAN sun kara jaddada kudurin bunkasa cikakkiyar hadin gwiwa bisa manyan tsare tsare

2023-07-14 10:43:25 CMG Hausa

Kasar Sin da kungiyar hadin gwiwar kasashen kudu maso gabashin Asiya ko ASEAN, sun kara jaddada kudurin su na bunkasa cikakkiyar hadin gwiwa bisa manyan tsare tsare, yayin taron ministocin waje da ya gudana a jiya Alhamis.

Da yake jawabi yayin taron, darakta a ofishin hukumar kula da harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce sassan biyu sun amince su yi aiki tare, domin aiwatar da sharudda, da ka’idojin dake kunshe cikin yarjejeniyar kawance, da hadin gwiwar yankin su ko TAC a takaice, tare da fadada cin gajiyar kawancen su daga dukkanin fannoni, da bude hanyar ingiza kyakkyawar makwaftaka ta dogon lokaci, ta yadda za a kai ga samun ci gaba da wadatar bai daya.

Taron na wannan karo ya hallara ministocin wajen kasashe mambobin kungiyar ASEAN, da wakilai masu sanya ido a kungiyar da kuma babban sakataren ta.

Har ila yau, yayin taron, Wang Yi ya gana da ministocin wajen kasashen Indonesia, da Brunei, da Singapore, da Vietnam, da Rasha da kuma Australia.   (Saminu Alhassan)