logo

HAUSA

MDD: Rikice-rikicen duniya sun jefa mutane sama da miliyan 122 cikin yunwa

2023-07-13 10:01:21 CMG Hausa

Tun daga shekarar 2019 ne mutane sama da miliyan 122 ke cikin yunwa a dalilin rikice-rikice da duniya ta ke fama da su na shekaru da dama. In ji wani sabon rahoto da hukumomin majalisar dinkin duniya suka fitar a ranar Laraba.

Rahoton 2023 na yanayin wadatar abinci da ababe masu gina jiki a duniya (SOFI) ya ce, annobar COVID-19, da munanan yanayi a duniya, da rikice-rikice na duniya, ciki har da wanda ya fara a bara tsakanin Rasha da Ukraine, a hade sun kara yawan mutanen da ke fuskantar yunwa a duniya zuwa kusan miliyan 735 a shekarar 2022. Adadin da ya kasance miliyan 613 a shekarar 2019. (Yahaya)