logo

HAUSA

Wang Yi: Hadin gwiwar Sin da Rasha da Indonesia na taimakawa ga wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin

2023-07-13 10:31:09 CMG Hausa

Babban jami'in diflomasiyyar kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin, da Rasha da Indonesia za ta taimaka wajen inganta tsarin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, baya ga inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin baki daya.

Wang, darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, ya bayyana a yayin ganawar bangarorin uku da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da na Indonesiya Retno Marsudi cewa, a matsayinsu na wakilan kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa kuma muhimmin mambobin kungiyar 20, mu’amala da hadin gwiwa a tsakaninsu ya dace da moriyar kasashen uku.

A nasu bangare Lavrov da Marsudi sun bayyana ra'ayoyinsu game da halin da ake ciki a duniya da ma shiyya-shiyya.

Jami’an sun yi imanin cewa, taron wani yunkuri ne mai fa'ida na gudanar da tattaunawa da musayar ra'ayi tsakanin sassan biyu, wanda ke wakiltar ra'ayinsu game da kiyaye yankin tsakiyar ASEAN da tsarin kasashen kungiyar ASEAN. Sun kuma amince su ci gaba da tattaunawa a kan wannan batu. (Ibrahim Yaya)