logo

HAUSA

90% na kananan yaran dake shiyyar arewa maso gabashin kasar Najeriya marayu ne sakamakon rikice- rikice

2023-07-13 09:27:46 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa rikice-rikicen da yankin gabashin kasar ya shafe shekaru a cikin ya yi sanadiyar mayar da dubban kananan yara marayu, bayan an hallaka iyayen su.

Babban sakatare a ma`aikatar lura da ayyukan jin kai da bada agajin gaggawa na tarayyar Najeriya Dr. Nasir Sani Gwarzo ne ya bayyana hakan jiya Laraba 12 ga wata a birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin wakilan kwamatin tsaro na majalissar dinkin duniya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Dr. Nasir Sani Gwarzo ya ce da yawa daga cikin wadannan kananan yara suna karkashin kulawar hukumomi ne a Najeriya, inda ake kula da harkokin walwalar su da kuma kokarin samar masu rayuwar mai inganci.

Ya ce yawaitar irin wadannan kananan yara da suke cikin hatsari bayan rashin iyaye, ya yi matukar jan hankulan hukumomin kasa da kasa da majalissar dinkin duniya da kuma kungiyar dake fafutukar kare kananan yara daga fadawa hannun ’yan ta’adda.

Dr. Nasir Sani Gwarzo ya ci gaba da bayanin cewa lokaci ya yi da ya kamata a samu ayyukan hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da sauran hukumomin ba da agaji na majalissar dinkin duniya wajen tattaunawa tare da fito da wani tsari sahihi da zai yayewa irin wadannan kananan yara damuwar da suke ciki.

Babban sakataren ma’aikatar ayyukan jin kai da bada agajin gaggawa ta tarayyar Najeriya ya shaidawa wakilan kwamitin tsaron na majalissar dinkin duniya cewa, ma’aikatar ta yi namijin kokari sosai wajen amfani da tsare-tsare da dabarun zamani da duniya ke amfani da su wajen maido da  kananan yara da aka samu cetowa daga hannun ’yan ta’adda a shiyyar arewa maso gabashin kasar zuwa cikin al’umma.

Ya ce duk da hakan irin wadannan kananan yara suna fuskantar hatsari sosai sakamakon yawan nakiyoyin da aka daddasa a wurare daban daban dake shiyyar.

Da take nata jawabin, jagorar ayarin majalissar dinkin duniyar Mrs. Vanessa Frazier ta ce saboda mahimmancin da majalissar ta dorawa batun kananan yara ne ya sanya ayarin zuwa Najeriya domin kawo dauki kan yadda za a kawo karshen matsalolin da kananan yara ke cin karo da su sakamakon rikice-rikicen da ake samu a kasar musamman ma a yankin arewa maso gabas.

Ha’ila yau ta ce zuwan su Najeriya zai ba su cikakken haske a kan irin kokarin da gwamnatin kasar ke yi da kuma sauran kungiyoyin agaji na kasa da kasa wajen tallafawa rayuwar irin wadannan kananan yara.

Daga bisani ta yaba matuka bisa rawar gani da gwamnatin kasar ta yi wajen bi sau da kafa dokoki da sharudodin kare hakkin kananan yara na majalissar dinkin duniya. (Garba Abdullahi Bagwai)