logo

HAUSA

Rahoton UNFPA ya nuna yadda mata masu asali daga Afirka ke fuskantar wariya a fannin kiwon lafiya a Amurka

2023-07-13 11:39:28 CMG Hausa

Wani sabon rahoto da asusun kula da yawan al’umma na MDD UNFPA ya fitar, ya nuna yadda cikin tsawon lokaci, mata da ’yan mata masu asali daga Afirka ke fuskantan wariya a fannin kula da lafiya a sassan arewaci da kudancin nahiyar Amurka, lamarin da ya jima yana jefa rayukansu cikin hadari musamman a lokacin haihuwa.

Rahoton wanda UNFPA ya fitar a jiya Laraba, ya ce matan da lamarin ke shafa na gamuwa da kalubale ta fuskar wayar da kai game da kiwon lafiya, da rashin lura da su yayin tsara manufofi, da hidimomin da ake bukata yayin haihuwa. 

Kaza lika rahoton ya yi nuni da cewa, sau da yawa ana cin zarafin mata masu asali daga Afirka ta hanyoyin hantara da muzgunawa ta zahiri, kana a kan hana su damar samun ingantacciyar kulawa, ko hana su magungunan kashe radadin ciwo. Sakamakon hakan a cewar rahoton, wannan rukuni na mata kan gamu da matsaloli, da hadurra yayin goyon ciki, ko jinkirin samun kulawa a asibiti, wanda hakan kan kai ga rasuwar wasu.

Bugu da kari, a wuraren da ake da cikakkun alkaluman bayanai na abubuwan dake faruwa, an lura cewa akwai wagegen gibi tsakanin adadin mata bakaken fata dake rasuwa sakamakon haihuwa, idan an kwatanta da takwarorinsu fararen fata musamman a Amurka, inda kiyasin mata bakaken fata daka iya rasa rayukansu yayin haihuwa, ya ninka na takwarorin su fararen fata har sau 3.   (Saminu Alhassan)