logo

HAUSA

Me ya sa taron kolin NATO ya sake shafawa kasar Sin bakin fenti?

2023-07-13 10:49:11 CMG Hausa

An kammala taron kolin kungiyar tsaro ta NATO a birnin Vilnius, fadar mulkin kasar Lithuania jiya Laraba, agogon kasar. A sanarwar hadin gwiwar taron da aka fitar, an ambaci kasar Sin fiye da sau goma, kuma an sake bayyana cewa, kasar Sin ta kasance babban kalubale ga tsaron yankin Turai da tekun Atilantika.

Bisa jadawalin kungiyar da aka tsara, ya kamata a tattauna halin da ake ciki a kasar Ukraine da kara yawan mambobin kungiyar a yayin taron kolin, amma me ya sa aka sake shafawa kasar Sin bakin fenti? A gaskiya wannan ba abin mamaki ba ne.

Sanin kowa ne cewa, kungiyar tsaro ta NATO ita ce babbar kawancen soji a duniya, kuma babban abin da ke kara tabbatar da wanzuwarta, shi ne samun abokan gaba, kuma daga muhimman takardun da suka shafi kungiyar, an lura cewa, ta kan zabi abokan gaba bisa bukatun kasar Amurka. Bayan da gwamnatin Joe Biden ta fara aiki, sai ta yi kuskure ta mayar da kasar Sin a matsayin abokiyar gogayya mafi muhimmanci, kuma ta bukaci kungiyar NATO da ta shiga shirinta na Indiya da tekun Pasifik. A karkashin irin wannan yanayi ne, kungiyar NATO ta kara nuna kiyayya ga kasar Sin, inda ta mayar da kasar Sin a matsayin babban kalubalenta, ta yadda za ta yi amfani da wannan manufa wajen tsoma baki a cikin harkokin yankin Asiya da tekun Pasifik. (Jamila)