logo

HAUSA

An mayar da ’yan Najeriya 146 gida daga jamhuriyar Nijar

2023-07-13 10:32:12 CMG Hausa

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce an mayar da wasu ’yan kasar su 146 gida daga jamhuriyar Nijar. NEMA ta ce mutane wadanda ke hanyarsu ta zuwa sassan kasashen Turai domin ci rani, sun makale a wasu kasashe Afirka da ake yada zango, kafin daga bisani su amince don radin kan su a mayar da su gida, karkashin shirin hukumar kasa da kasa mai lura da ‘yan ci rani ko IOM.

Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Laraba, shugaban hukumar NEMA reshen jihar Kano dake arewacin Najeriya Nuraddeen Abdullahi ya ce, mutanen da aka mayar Najeriya sun sauka ne a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano dake jihar ta Kano, sun kuma hada da maza 56, da mata 39, da kananan yara 51, da suka fito daga jihohin kasar daban daban. (Saminu Alhassan)