logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a ba da fifiko kan wadatar abinci a ajanda na kasa da kasa

2023-07-13 10:40:21 CMG Hausa

A ran 12 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Dai Bing, ya bayyana cewa, yadda za a daidaita wadatar abinci, da raya birane da kauyuka, wani muhimmin batu ne da kasashe ke fuskanta. Ya kamata kasashen duniya su ba da fifiko kan samar da abinci a ajanda na kasa da kasa, su yi cikakken amfani da rawar da hukumar abinci da aikin noma ta majalisar dinkin duniya ke takawa, tare da tallafa wa kasashe wajen lalubo hanyoyin da za su dace.

Dai Bing ya bayyana haka ne a wajen taro na musamman kan fitar da rahoton 2023 na yanayin wadatar abinci da ababe masu gina jiki a duniya. (Yahaya)