logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Fitar Da Sakamakon Binciken Fashewar Bututan Nord Stream Da Wuri

2023-07-12 20:52:34 CMG Hausa

Mataimakin wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira da a gaggauta fitar da sakamakon bincike don gane da fashewar bututan iskar gas na Nord Stream da ta faru kusan watanni 10 da suka wuce.

A cewar Geng Shuang, kasashen da batun ya shafa sun shafe lokaci suna nazari kan batun, amma har yanzu ba a fitar da wata kwakkwarar sanarwa ba.

A cewarsa, fashewar bututan ta auku ne yayin da rikicin Ukraine ke wakana, yana mai cewa bangarorin da abun ya shafa sun yi nazari tare da fassara daban-daban game da lamarin. Ya kara da cewa, suna kira ga dukkan bangarori da kada su siyasantar da binciken, kuma kada su yi amfani da shi a matsayin wata dama ta kitsa gutungwilar siyasa.

Geng ya kuma jaddada cewa, Rasha daya ce daga cikin bangarorin da batun ya shafa, don haka duk wani bincike mai ma’ana ba tare da bangaranci ba, na bukatar tuntuba da hadin gwiwa da Rasha. (Fa’iza Mustapha)