logo

HAUSA

MDD: Dubban mutane ke tserewa tarzomar yankin Darfur na Sudan zuwa Chadi

2023-07-12 10:13:40 CMG Hausa

A jiya Talata ne ma’aikatan jin kai na majalisar dinkin duniya suka bayyana cewa dubban jama'a a yankin Darfur na kasar Sudan a kowace rana sun zabi su yi rayuwar 'yan gudun hijira a kasar Chadi saboda tashin hankali da kasarsu take ciki.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya OCHA ya ce hukumar samar da abinci ta duniya WFP tana kara kaimi wajen tallafawa sabbin zuwa da yawancinsu ke dauke da raunuka. Ya zuwa yanzu dai, hukumar ta kai agajin abinci da ababen gina jiki ga ‘yan gudun hijira sama da 150,000 a kan iyakar Chadi da Sudan. (Yahaya)