logo

HAUSA

Masuntan Fukushima na ci gaba da adawa da zuba ruwan dagwalon nukiliyar cikin teku

2023-07-12 13:47:55 CMG Hausa

Kungiyoyin masunta a yankin Fukushima sun fada jiya Talata cewa, suna ci gaba da adawa da shirin zuba ruwan dagwalo daga gurbatacciyar tashar makamashin nukiliya zuwa cikin teku, duk da cewa hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA ta ba da tabbaci kan shirin.  

Kamfanin dillancin labarai na Kyodo ya ce, ministan tattalin arziki, kasuwanci da masana'antu na Japan Yasutoshi Nishimura, ya yi wa hukumar kula da ayyukan masunta ta Fukushima da ke arewa maso gabashin Japan bayani game da rahoton hukumar ta IAEA na baya-bayan nan game da shirin zuba ruwan dagwalon nukiliya a teku, a wani yunkuri na neman fahimtarsu yayin da kasar Japan ta yi niyyar fara zubar da ruwan a wannan yanayin zafi.

A ranar 11 ga wata, wata tawagar hana zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku da ya kunshi 'yan jam'iyyar adawa a kasar Koriya ta Kudu da ke ziyara a Japan da wasu 'yan kasar Japan sun gudanar da wani gangami a gaban babbar kotun birnin Tokyo, inda suka yi kira ga gwamnatin kasar Japan, don soke kudurin zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku. (Yahaya)