logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Bauchi za ta fara aikin rabon gidajen sauro har miliyan 4.4 ga magidanta dake jihar

2023-07-12 09:32:23 CMG Hausa

Hukumar yaki da zazzabin cizon sauro da tarin fuka da kuturta ta jihar Bauchi a arewacin Najeriya BACATMA ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata domin fara aikin rabon gidajen sauro ga magidanta dake jihar.

Shugaban hukumar Dr. Sani Mohammed Dam-bam ne ya tabbatar da hakan jiya Talata a garin Bauchi yayin da yake ganawa da manema labarai a game da shirin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Tun dai a karshen watan jiya ne gwamnan jihar ta Bauchi Sanata Bala Muhammad ya kaddamar da shirin fara tsara rabon gidajen sauro ga al’ummar jihar, inda tun daga wancan lokaci aka fara rabar da katinan sheda ga magidantan da aka shigar cikin jadawalin mutanen da za su amfana.

Dr. Sani Muhammad Dam-bam ya ce, aikin rabon gidajen sauro za a fara shi ne daga ranar 13 ga wannan watan na Yuli, kuma za a shafe mako guda ana aikin.

Shugaban hukumar ta BACATMA ya tabbatar da cewa an kashe a kalla Naira biliyan 8 wajen samar da gidajen sauron, wanda aka tsara magidanta biyu a kowanne gida dake fadin jihar Bauchi baki daya za su amfana.

Daga bisani Dr. Sani Muhammad Dam-bam ya nemi hadin kan al’ummar jihar kamar haka, 

“Muna son al’umma su saka mu a addu’a domin wanann aiki ya tafi daidai. Na biyu muna son al’umma su taimaka mana a saka ido domin kada a karkatar da wadannan gidajen sauro. Muna son a taimaka a saka ido domin tabbatar da ganin an kai su inda ya kamata kuma bata gari ba su samu dama sun karkatar da shi ba.”

Rahoton hukumar yaki da cutar malaria ta duniya na 2022, ya nuna cewa ana samun matsalolin cutar zazzabin cizon sauro har miliyan 66 a duk shekara a Najeriya.

Sannan kuma a binciken da hukumar dake nazartar cutar malaria ta tarayyar Najeriya ta fitar ya nuna cewa, kaso 44 na wadanda suke kamuwa da zazzabin cizon sauro a jihar Bauchi kananan yara ne ’yan kasa da shekaru 5 da haihuwa, kuma a Najeriya jihar ta Bauchi ita ce ke da kaso 36 na matsalolin zazzabin cizon sauro da ake samu a rahoton da aka fitar na shekara ta 2021. (Garba Abdullahi Bagwai)