logo

HAUSA

Kungiyar NATO ta gaza ba da jadawalin kasancewar Ukraine mamba a taron kolin kungiyar

2023-07-12 10:09:26 CMG Hausa

Shugabannin kungiyar tsaro ta NATO, sun gaza tsara jadawalin yadda kasar Ukraine za ta kasance mamba a kungiyar, a ranar farko na taron kungiyar a Vilnius, babban birnin kasar Lithuania.

Da yake magana a wani taron manema labarai, babban sakataren kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg ya ce, kawayen kungiyar sun amince da wasu kunshin abubuwa guda uku da za su kara kusanto Ukraine shiga NATO. Sai dai kuma ya fayyace cewa, za a baiwa Ukraine goron gayyata na shiga cikin kawancen ne, lokacin da kawayen kungiyar suka amince kuma aka cika dukkan sharuda da suka wajaba.

A jawabinsa shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, wannan abu ne da ba a taba ganin irinsa ba kuma hankali ma ba zai dauka, a ce ba a tsayar da lokacin da za a baiwa kasarta damar zama mambar kungiyar ba. Ana dai sa ran Zelensky zai halarci taron kaddamar da sabuwar majalisar NATO da Ukraine da zai gudana Larabar nan.

Rahotanni na cewa, an samu rarrabuwar kawuna tsakanin mambobin kungiyar, kan yadda za a baiwa kasar Ukraine damar shiga kungiyar. Yayin da wasu mambobin kasashen gabashin Turai ke matsa lamba kan daukar kwararan matakai game da lokacin da Ukraine za ta shiga kungiyar, su kuwa kasashen Amurka da Jamus sun ki su ke komai kan wannan batu. (Ibrahim Yaya)