logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa tawagar MINUSCA a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

2023-07-12 11:28:21 CMG Hausa

MDD ta yi tir da harin da aka kai wa tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato (MINUSCA) a ranar Litinin din da ta gabata, harin da ya yi sanadin mutuwar wani sojan kiyaye zaman lafiya dan kasar Rwanda.

A cikin wata sanarwar da suka fitar, mambobin kwamitin sulhun sun yi kira ga gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da ta gaggauta gudanar da bincike kan harin bisa goyon bayan tawagar ta MINUSCA, domin gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kuliya, tare da sanar da sojojin kasar dake ba da gudummawa game da ci gaban da aka samu.

Mambobin kwamitin sun jaddada cewa, hare-haren da ake kaiwa dakarun wanzar da zaman lafiya, na iya zama laifukan yaki bisa dokokin kasa da kasa. (Ibrahim Yaya)