logo

HAUSA

Taron ECOWAS karo na 63 ya fitar da sanarwar da ya bukaci Mali da ta saukaka ayyukan tura dakarun ECOWAS

2023-07-11 11:36:32 CMG Hausa

A ranar 10 ga watan Yuli ne kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fitar da sanarwar taron koli karo na 63 da aka gudanar a kasar Guinea-Bissau a ranar 9 ga watan Yuli. Sanarwar ta ce ya kamata kasashen Mali, Guinea da Burkina Faso da ke kan matakan rikon kwarya a yankin, su bi jadawalin mika mulki da aka amince da su a baya, tare da maido da tsarin mulki da zabe a shekarar 2024.

Ecowas ta yaba da gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar Mali a matsayin wani muhimmin mataki na sake tabbatar da tsarin mulkin kasar, kuma hukumar ta ECOWAS za ta ba da tallafin tsaro da jin kai ga kasashen uku domin kammala mika mulki cikin kankanin lokaci.

Hukumar ta ECOWAS za ta ba da shawara a cikin kwanaki 90 a kan cikakken tsarin mayar da martani game da janyewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali da kuma kasancewar dakarun kasashen waje masu zaman kansu a yankin, sannan ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin Mali da su saukaka aikewa da kayan aiki da jigilar tawagar mambobin kungiyar ECOWAS. (Yahaya Babs)