logo

HAUSA

NBS: Jihohi 28 ne a tarayyar Najeriya ba su samu kulawar masu zuba jari daga waje ba a zangon farko na 2023

2023-07-11 10:33:36 CMG Hausa

A cikin wani rahoto da ta fitar jiya Litinin, hukumar kididdigar tattalin arzikin kasa a tarayyar Najeriya NBS  ta ce jihohi 28 ne daga cikin 36 a tarayyar Najeriya ba su samu kulawar da ta kamata ba daga masu saka zuba jari ’yan kasashen waje a zangon farko na 2023.

Kamar dai yadda yake kunshe cikin rahoton da hukumar ta fitar kuma aka rabawa manema labarai a birnin Abuja, rahoton ya nuna cewa duk da an samu karuwar shigowar kudade daga waje zuwa kasar amma bai kai abun da ake hasashe ba sosai.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Hukumar kididdigar tattalin arzikin ta tarayyar Njeriya ta tabbatar da cewa adadin kudade da kasar ta samu daga masu saka jari a zangon farko na 2023 ya karu da kaso 6.78 cikin dari.

Rahoton hukumar ya ce jihar Legas ce ta fi jan hankalin masu zuba jari ’yan kasashen waje, sai kuma birnin Abuja da Akwa Ibom da Adamawa da Ogun.

Sauran su ne jihohin Niger da Ondo da kuma Ekiti.

Rahoton ya nuna cewa a matsayinta na cibiyar hada-hadar kasuwancin kasar, jihar Legas ta yi sanadin shigowar dala miliyan 704.87 kwatankwacin kaso 62 cikin dari na adadin kudaden da kasar ta samu daga masu zuba jari ’yan kasashen waje.

Sai kuma birnin Abuja da take biye mata da dala miliyan 410.27 wanda yake wakilta kaso 36 na adadin kudaden da Najeriya ta samu daga ’yan kasuwar kasashen waje.

Ko me masana harkokin tattalin arzikin kasa za su ce game da wannan rahoto?

Farfesa Aliyu Tahir malami ne a sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar Bayero dake Kano a arewacin Najeriya.

“Wannan rahoto ban yi mamakinsa ba saboda na daya dai ka ga maganar tsaro yana da matukar mahimmanci, babu wanda zai dauko dukiyarsa ya kawo ta inda ba a da tabbas na harkokin tsaro, sannan na biyu gwamnati tana yin dokoki da kudure- kudure amma sai ya zamana wadannan dokoki suna cin karo da juna, to mutum ya zo ya baje koli ya baje kasuwa kuma ka ga shi bako ne yana kula da me canjin duniya take faruwa nan kuma a zo yau dala ta karu gobe ta ragu irin wanann yana kawo tasgaro, dole sai gwamnati ta natsu ta san cewa doka kafin a yi ta a natsu a san cewa abu ne da zai dauki lokaci kafin a canja domin wannan zai baiwa masu saka jari kwarin gwiwa.”

Daga cikin bangarorin zuba jari a Najeriya sun hadar da makamashi, aikin gona da sha’anin ma’adanai. (Garba Abdullahi Bagwai)