logo

HAUSA

Me ya sa kasashen yamma suka yi shiru kan shirin Japan na zubar da ruwan tagwalon nukiliya a cikin teku?

2023-07-11 13:46:33 CMG Hausa

Kawo ran 10 ga watam Yuli, wato kusan mako guda ke nan bayan da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA a takaice, ta fitar da rahoton game da shirin kasar Japan na zubar da ruwan tagwalon nukiliyara Fukushima a teku. A wannan lokaci, kasashen duniya kamar kasashen tsibiran Pacific, da Philippines, da Indonesia, da Afirka ta Kudu, da Peru, da Sin da Koriya ta Kudu sun nuna fushi sosai ga shirin Japan na zubar da gurbataccen ruwan a teku, amma a bangare nasu, abin da kasashen yamma, kamar kasar Amurka suka yi ya sha bamban kwarai.

Me ya sa wasu kasashen yamma ba su nuna damuwa, har ma sun “kwantar da hankulansu” da shirin Japan din na zubar da gurbataccen ruwan nukiliya a cikin teku ba?

A cewar jaridar Los Angeles Times, a cikin shekarun 1940 da 1950, Amurka ta gudanar da gwaje-gwajen nukiliya har sau 67 a tsibiran Marshall dake cikin tekun Pacific. Bugu da kari, a baya, Amurka ta taba yin jigilar gurbatacciyar kasar nukiliya da aka samu a wurin gwajin nukiliya dake jihar Nevada zuwa tsibiran Marshall, sannan ta zubar da irin wannan gurbataciyyar kasar nukiliya a tsibirin Marshall kai tsaye. Wannan na iya zama amsar dalilin da ya sa Amurka ta dade da yarda da shirin Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku, domin tana daya daga cikin wadanda suka fara gurbacewar teku.

Ban da wannan, a ganin Amurka, batun tsaron nukiliya ya kasance kamar wani abun da ta iya yin musayar moriya. Wasu bayanan nazari sun yi nuni da cewa, bayan karshen yakin duniya na biyu, makamashin nukiliya shi ne makami ne da Amurka take amfani da shi wajen mallakar Japan. A daya bangare kuma, shi wani muhimmin makami ne ga Japan da take jinginawa da kuma dogara da kasar Amurka. 

Amurka ta dade tana ikirarin kare “hakkin bil’adam” na daukacin al’umma. Amma a hakika dai, tana kula da mulkin danniya nata kawai, maimakon hakkin bil’adam, kuma tana kula da moriyar siyasa ta radin kanta kawai, maimakon hakkin jama’a.

Tekun Pacifik teku ne na daukacin bil’adama na duk duniya baki daya. Kamata ya yi gwamnatin Japan ta yi biyayya ga kiraye-kirayen adalci na bangarori daban daban, sannan ta dakatar da shirinta na zubar da gurbataccen ruwan nukiliya a cikin teku nan da nan. Wadancan kasashen yammacin duniya da har yanzu suke shiru, kada su zama abokan hulda na wannan shiri. (Safiyah Ma)