logo

HAUSA

Shugaba Mohamed Bazoum ya gana da wata tawagar likitocin Nijar da Senegal domin kamfen tiyatar zuciya

2023-07-11 10:10:24 CMG Hausa

A ranar jiya Litinin 10 ga watan Yulin shekarar 2023, shugaban kasar Nijar ya tattauna tare da wata tawagar da ke kunshe da kwararrun likitocin kasashen Nijar da Senegal a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai.

Daga birnin Yamai din abokin aikinmu Mamane Ada ya turo mana da wannan rahoto.

Batutuwan karfafa da inganta bangaren kiwon lafiya tsakanin kasashen Nijar da Senegal su ne tsakiyar ita wannan ganawa tsakanin shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum da wata tawagar hadin gwiwa da ke kunshe da likitocin kasashen biyu a hedkwatar babban birnin kasar Nijar. Ita wannan tawaga ta hada kwararrun likitocin zuciya, haka zalika tattaunawar tare da shugaba Bazoum ta tabo maganar kaddamar da wani kamfen tiyatar zuciya a babban asibitin misali HGR da ke nan birnin Yamai.

Wanda kuma, wannan kamfe yake cikin tsarin hadin gwiwar aiki, wanda ta dalilinsa tawagar likitocin kasar Senegal ta zo babban birnin kasar ta Nijar domin yiwa kananan yara da ke fama da ciwon zuciya. Wannan aiki ya soma tun daga ranar jiya Litinin 10 ga watan Yuli har zuwa ranar Alhamis 13 ga watan Yulin shekarar 2023, in ji darekta-janar na babban likitar misali HGR, forfesa Eric Adehossi jim kadan bayan ganawarsu tare da shugaban kasar Nijar.

A cewar jami’an ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa, ciwon zuciya na daya daga cikin manyan cututtuka na wannan lokaci da suka fi haddabar al’ummar Nijar, musamman ma kananan yara, Zuwan wadannan likitocin kasar Senegal, ya kasance wani abin alheri ga wadanda suke fama da ciwon zuciya. A cewar wasu alkaluman baya bayan nan na kungiyar kiwon lafiya ta duniya OMS na shekarar 2020, mace-macen ciwon zuciya a Nijar sun cimma kashi 5.12 cikin 100 na jimillar mace-macen mutane.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.