logo

HAUSA

Sin ta sake yin kira ga Japan da ta dakatar da shirin zuba ruwan dagwalon nukiliya cikin teku

2023-07-11 09:46:46 CMG Hausa

A ranar Litinin din nan a gun taron kwamitin kare hakkin bil Adama na MDD karo na 53 da ke gudana, kasar Sin ta sake yin kira ga kasar Japan da ta dakatar da shirinta na zuba ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku.

Kwamitin kare hakkin dan Adam na majalisar dinkin duniya a ranar Litinin ya amince da sakamakon nazarin da duniya ke gudanarwa a kai a kai (UPR) na kasar Japan. Wani jami’in diflomasiyyar kasar Sin da ya yi jawabi a wajen tattaunawa kan sakamakon UPR na kasar Japan, ya jaddada cewa, kasar Sin ta sake yin kira ga kasar Japan da ta dakatar da shirinta na zuba ruwan dagwalon nukilya a cikin teku.

Jami'in diflomasiyyar na kasar Sin ya bukaci Japan da ta yi watsi da shirin bisa tsarin kimiyya, aminci da gaskiya, tare da hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, wajen tsara tsarin sa ido na kasa da kasa na dogon lokaci, wanda zai shafi makwabtan Japan da sauran masu ruwa da tsaki nan ba da jimawa ba. (Yahaya)