logo

HAUSA

Bankin duniya na kashedi kan matsalar muhalli dake ta da hankali sosai a Nijar

2023-07-10 11:29:37 CMG Hausa

Nijar na kasa ta 152 bisa 180, bisa kuzarin muhalli na YALE, a cewar rahoton binciken muhallin kasashe AEP na bankin duniya. Wanda ya nuna cewa matsalar muhalli a Nijar na tada hankali sosai. Kuma, hakan na iya kawo cikas ga tsaron abinci, da hijirar mutane a nan gaba.

Daga birnin Yamai, Mamane Ada ya duba mana wannan rahoto.

 

Shi dai wannan rahoto na duba muhimman kalubale na muhalli da ke iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki mai karko a Nijar. Wannan nazarin ya gabatar da shawarwari tamkar wasu bukatu domin fuskantar mataslar.

Nazarin AEP ya rataya kan muhimman abubuwa guda uku, su ne lalacewar kasa, kashe itatuwa da lalata dazuzzuka, da kuma sauyin yanayi. Adadin kashe itatuwa ya wuce matsakaicin lalata dazuzzuka, da kawo barazana ga lafiyar nau’o’in itacen gida dake da muhimmanci ga tattalin arziki daban daban. Haka kuma sauyin yanayi zai iya kawo illa ga noma, ga albarkatun ruwa da lafiyar al’umma.

Domin warware wadannan matsaloli a cewar rahoton, yana da kyau a kafa wani tsarin hada dukkan batutuwan gaggawa domin samar da mafita mai karko. Rahoton ya bayyana cewa halartar matasa da mata cikin aiwatar da ayyuka za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen kyautata jin dadin rayuwar al’umma. Game da lalacewar kasa, rahoto ya yi bayanin cewa filayen noma sun karu fiye da shekaru 20 na baya bayan nan dalilin karuwar al’umma cikin sauri, ga ayyukan noma maras dacewa, rashin kula da ruwa, zafin rana na dadada karuwa da hasashen yanayi maras tabbas, dukkan wadannan abubuwa sun hana samun damina mai albarka a cikin yankuna da dama da kuma kawo wani cikas ga wuwaren noma, ganin cewa matsalar tsaron abinci na zama barazana ga kashi 1/3 na al’ummar Nijar, a cewar wannan rahoto.

Daga karshe, rahoton ya ambato kokarin da hukumomin kasar Nijar suke yi wajen kiyaye da kare muhalli da sauyin yanayi, inda tun a shekarar 1980, kasar ta kafa matakan farfado da kasa, tare da bada kawarin gwiwa ga shirin taimakawa sake farfado hallitu RNA, ta amfani da hanyoyin kyautata noma, da amfani da fasahohin zamani na tattara ruwa, wannan ya taimaka kyautatuwar kasa da ciyayi, musamman ma a yankunan Maradi, Zinder da Tahoua. A cewar rahoton fiye da kashi 6 cikin 100 na filaye sun yi fama da lalacewa a tsawon shekarar 2001 zuwa 2015.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.