logo

HAUSA

Hadarin mota kirar bas da babbar mota ya yi ajalin mutane 20 a kudu maso yammacin Najeriya

2023-07-10 11:08:14 CMG Hausa

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa, mutane 20 ne suka mutu bayan da wata motar bas ta daki wata babbar motar tipper a ranar Lahadi a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Bas din dauke da mutane 20, ta afkawa wata motar tipper wadda ke makil da yashi a kusa da garin Mowo da ke kan hanyar Legas zuwa Badagry a jihar, in ji kakakin LASTMA, Taofiq Adebayo, wanda ya tabbatar wa manema labarai hadarin a Legas.

A cewar Adebayo, bas din ta kubcewa direban ya rasa yadda zai yi, yayin da ya ga wata babbar mota a gabansa a lokacin da yake kokarin wuce tipper da ke dauke da yashi.

Jami’in ya ce “Bas din ta yi karo da tipper, inda mutane 20 da ke cikin bas din suka mutu nan take, ciki har da fasinjoji 18 tare da direban bas din da yaron aikinsa,” ya ce ba a bin da ya sami direban tipper. An kuma ajiye gawarwakin mutanen a dakin ajiyar gawa. (Yahaya)