logo

HAUSA

Masar za ta karbi bakuncin taron makwabtan Sudan a kokarin kawo karshen rikici

2023-07-10 10:09:02 CMG Hausa

Kasar Masar ta sanar da shirin karbar bakuncin taron koli ga kasashen dake makwabtaka da kasar Sudan ranar Alhamis mai zuwa, domin lalubo hanyoyin warware rikicin kasar ta Sudan cikin lumana.

Sanarwar da fadar shugaban Masar ta fitar ta ce, shugabannin da ke halartar taron za su tattauna batun samar da ingantattun hanyoyin da za a bi a yankin da ma kasashen duniya domin warware rikicin da kuma irin illar da rikicin ke yi wa kasashen da ke makwabtaka da Sudan.

Sudan dai na fama da tarzoma tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai na gaggawa a fadin kasar tun daga ranar 15 ga watan Afrilu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 3,000, yayin da wasu a kalla 6,000 suka jikkata, a cewar ma'aikatar lafiya ta kasar Sudan.

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa, fiye da mutane miliyan 2.8 ne suka rasa matsugunansu, akasari na cikin gida, tun bayan barkewar rikici a Sudan, makwabciyar kudancin Masar. (Yahaya)